Ciyaman din APC na jihar Ondo ya bada gargadi
– Shugaban jam’iyyar APC na jihar Ondo ya bada gargadi
– Isiac Kekemeke ya roki yan jam’iyyar su amshi sabbin shigowa daga PDP
– Shugaban ya nemi yan jam’iyyar su goya ma jam’iyyar baya
Ciyaman din jam’iyyar APC na jihar Ondo, Isiac Kekemeke, ya roki mambobin jam’iyar jihar da su daina batanci ga sabbin shigowa jam’iyyar a shafukana sada zumunta.
Today.ng ta ruwaito cewa Kekemeke ya bada gargadin shi ne saboda wasu yadda magoya bayan wasu yan takarar zaben gwamnan jihar dake tahowa suke zage zage akan junan su a shafukan sada zumunta.
KU KARANTA: Shugaban Buhari ya tattauna da shugabannin jam’iyyar APC
Kekemeke ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsar tsohon mai bada shawara akan shari’a na jam’iyyar PDP, MrOlusola Oke. Mr Olusola kuma ya bayyanar niyyar shi akan yayi takara akan jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar jihar ta Ondo ya bayyana Olusola a matsayin gogaggen dan siyasa wanda ya shahara wajen siyasa a jihar Ondo da kuma a kasa najeriya gaba ki daya.
Kekemeke ya bayyana cewa Olusola yayi aiki a wurare daban daban kuma ya taba zama dan majalisar tarayya kuma ya dade yana ba jam’iyyar APC gudunmuwa.
Shugaban jam’iyyar ya nemi da yan jam’iyyar su goya ma kowa jam’iyyar ta tsaida domin yaci nasarar cin zaben jihar.
A wani labarin kuma, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Cif John Oyegun, ya bayyana cewa zaben Rivers abun takaici ne. Ya bayyana wannan a jihar Alhamis 24 ga watan Maris.
The post Ciyaman din APC na jihar Ondo ya bada gargadi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.